Ba tare da bata lokaci ba ‘yan sanda suka mayar da martani ga harbin wanda aka yi a unguwar Vaughan, da ke da nisan kilomita 20 daga arewacin Toronto, kuma a take aka harbe dan bindigar.
An kwashi wadanda suka ji rauni zuwa asibiti. Tuni aka fara gudanar da bincike a kan dalilin harin. Babban jami’in dan sanda a garin ya ce jami’ansu sun ga tashin hankali saboda yadda suka tsinci gawarwaki a cikin gidajen da ke unguwar.
An kwashe mutanen da ke zaune a rukunin gidajen, amma kuma an ce bayan bincike za a mayar da su gidajensu.
Ba kasafai ake samun harbe-harben bindiga a Canada ba, to amma a watannin baya bayan nan ana kara samun hare haren bindiga a kasar.