MURIC ta bayyana shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin shugaba na kwarai wanda bai taba “satar ko kobo ba”.

Kungiyar kare hakkin musulmi ta MURIC, ta bayyana shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin shugaba na kwarai wanda bai taba “satar ko da kobo ba”.

MURIC ta bayyana hakan ne a lokacin da take taya shugaba Buhari murnar cika shekaru 80 a duniya.

KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Tarayya ta musanta zargin da wani tsohon ma’aikacin Twitter ya yi cewa kamfanin bai tattaunawa da gwamnatin Najeriya ba bayan dakatar da shi.

Kungiyar ta MURIC ta sake jaddada kiran da ta yiwa shugaban kasa a shekarar 2021 a matsayin ‘Uban Najeriya ta Zamani.

A wata sanarwa da Daraktan kungiyar Farfesa Ishaq Akintola yafitar, kungiyar ta bayyana cewa tsofaffin shugabannin kasar da
suka gabata sun zubar da kimar ofishinsu na shugaban kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *