Gwamnatin Tarayya ta musanta zargin da wani tsohon ma’aikacin Twitter ya yi cewa kamfanin bai tattaunawa da gwamnatin Najeriya ba bayan dakatar da shi.

Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, wanda ya musanta wannan ikirari, ya fitar da hujjojin tattaunawar da aka yi tsakanin kamfanin twitter da gwamnati.

Ministan ya yi wannan jawabi ne a karo na 13 na jerin taron fitar da nasarorin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu tsakanin shekarar (2015-2023) wanda ya kunshi ministar harkokin
mata, Paulen Tallen.

Idan za a iya tunawa, a ranar 4 ga watan Yunin 2021, gwamnatin Najeriya ta dakatar da ayyukan Twitter, sakamakon zargin kamfanin da yin barazana ga zaman lafiya da kuma hadin kan kasa.

KARANTA WANNAN LABARIN: MURIC ta bayyana shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin shugaba na kwarai wanda bai taba “satar ko da kobo ba”.

Sabanin ikirarin da tsohon ma’aikacin na Twitter ya yi, ministan ya ce an dade ana tattaunawa tsakanin Najeriya da Twitter bayan
dakatar da dandalin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *