Gwamnatin Kaduna ta fara sakin ababen hawan da aka kama

Hukumar kula zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kaduna KASTLEA, ta ce za ta saki dukkan baburan da ta kama a shekarar 2022, daga ranar Talata.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mukaddashin hukumar KASTLEA, Carla Abdulmalik, ta fitar ranar Lahadi a Kaduna.

Sai dai ta ce dole ne masu baburan da aka kama su biya tara tare da daidaita takardunsu.

Mukaddashin hukumar Marshall ya ce za a gudanar da shirin ne daga 20 ga watan Disambar 2022 zuwa 20 ga watan Janairu, 2023.

A cewar ta, za a gudanar da aikin tantance takardun ne a filin wasa na Ahmadu Bello, inda za a cike fom da kwafin takardun da masu su ke da shi tare da sanya hannu kan wani aiki.

Masu baburan da ba su yi rajista ba za su biya Naira 30,000.00 kowannensu sannan wadanda ba su da lambobi ko bayanai za su biya Naira 12,000.00 kowanne, jimillar Naira 42,000.00.

“Masu baburan da suka yi rajista za su biya Naira 20,000 da kuma Naira 3,700 don sabunta bayanai, jimillar Naira 23,700.

“Ana sa ran masu babura su gabatar da katin shaidar dan kasa, takardar sayen babur, bayanan rajista da kuma hotunan fasfo, kafin a sako musu baburan,” ta kara da cewa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *