DSS ta janye dakarunta da ta tura gadin Gwamnan Jihar Osun da gidan Gwamnatin Jihar.

Hukumar Tsaro ta (DSS) ta janye dakarunta da ta tura gadin Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke da gidan Gwamnatin Jihar da kuma Ofishin Gwamnan.

KARANTA WANNAN LABARIN: Mutane biyar sun rasa ransu bayan da wani dan bindiga ya bude wuta rukunin gidaje da ke Toronto a Canada.

Jita-jita dai ta yi kamari cewa hukumar ya yanke shawarar daukar matakin ne bayan Gwamnan ya zage ta.
To sai dai mai magana da yawun Gwamnan, Olawale Rasheed, a cikin wata sanarwa ya ce janyewar na da nasaba ne da ‘kishin’ da ake samu tsakanin jami’an ’yan sanda da na DSS din da aka tura
su yi gadin Gwamnan.

Rasheed ya ce matakin lamari ne da ya shafi hukumomin ’yan sanda da na DSS, ba Gwamnan ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *