‘Yan bindiga sun kwashe Gaba Daya mazajen wani gari a jihar Zamfara.

‘Yan bindiga sun kwashe daukacin mazajen garin Randa dake karamar hukumar Maru a Jihar Zamfara saboda bacewar bindigoginsu, yayin da suka yi sanadiyar mutuwar 20 daga cikin su.

Rahotanni sun ce mabiya wani gawartaccen ‘dan bindigar yankin da ake kira Lawali Damina ne suka aikata wannan aika aikan na kwashe mazajen wannan gari, cikinsu harda kananan yara saboda bacewar
bindigogin mabiyansa guda 2.

Bayanai sun ce wadannan bindigogi guda biyu sun bace ne lokacin da akayi arangama tsakanin magoyan bayan Damina da wasu abokan gabarsu akan wata budurwa.

A wannan yanki ne ‘yan bindiga ke sanya haraji da kuma gindaya sharidodi ga jama’a akan yadda zasu gudanar da harkokinsu na yau da kullum.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *