Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan tsohon shugaban jami’ar Ahmadu Bello.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sake jaddada matsayin gwamnatinsa na ganin an gudanar da tsaftacacen zabe mai ingancin da duniya zata amince da shi a watan Fabarairu, duk da hare haren da
batagari suke ci gaba da kaiwa a ofisoshin hukumar zaben.

Yace Babu wani dalili ko Uzuri ga hukumar zabe ta kasa INEC na Gaza yin zaben gaskiya a shekarar 2023.
Buhari ya shaidawa jami’an Cibiyar tabbatar da zaman lafiya dake Washington cewar, har yanzu yana kan bakarsa na ganin an samar da yanayi mai kyau da zai baiwa hukumar zaben damar gudanar da
karbabben zabe a shekara mai zuwa.

Shugaban ya bayyana hare haren da ake kaiwa ofisoshin hukumar zabe da cewa Wasu Yan tsiraru ne wadanda ba zasu iya shafar kimar zaben baki daya ba, yayin da yace an samu ingancin tsaro a wasu yankunan kasar Nan Kuma Hakan ba zai Hana INEC aikinta ba musamman zaben gaskiya.

A shekara mai zuwa shugaba Buhari zai kammala wa’adin mulkinsa na shekaru 8, abinda ke nuna cewar Najeriya zata samu sabon shugaban kasa daga cikin ‘yan takarar da suke ci gaba da karade sassan kasar domin neman goyan baya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *