Argentina Ta Lashe Kofin Duniya

Wannan shi ne karo na uku da Argentina ke lashe kofin gasar, na farko a shekarar 1978 sai a 1986.

Tawagar ‘yan wasan Argentina ta lashe kofin gasar kofin duniya a Qatar bayan da ta lallasa Faransa a bugun fenariti da ci 4-2.

Wasan ya kai bugun fenariti ne bayan da aka tashi da ci 3-3 duk da karin lokacin da aka yi.

Tun a farkon wasan, wato kafin a je hutun rabin lokaci, Argentina ta shiga gaban Faransa da ci 2-0.

Messi ne ya fara zura kwallo a ragar Faransa da bugun fenariti a minti na 23.

A minti na 36 kuma Di Maria ya kara wata kwallo ta biyu bayan wani gudun zari ruga da ‘yan wasan gaba na Argentina suka yi ciki har da Messi.

Sai dai Faransa ta samu bugun fenariti ita ma a minti na 78, inda Kylian Mbappe ya buga ya kuma ci.

Jim kadan bayan hakan Mbappe ya kara wata kwallo ta biyu, lamarin da ya kai wasan 2-2.

Sai dai Messi ya kara wata kwallo a karin lokacin da aka yi, kwallon da ta kai wasan 3-2.

Amma wata fenariti da aka ba Faransa, ta sa wasan ya koma 3-3 bayan da Mbappe ya buga.

Rabon da Argentina ta lashe kofin gasar tun a 1986, lokacin da kyaftin Diego Maradona ya jagoranci tawagar ‘yan wasan kasar.

Wannan kuma shi ne karo na uku da Argentina ke lashe kofin gasar, na farko a shekarar 1978 sai a 1986.

Faransa sau biyu tana lashe kofin gasar, a 1998 da 2018 da ta lashe a baya-bayan nan a Rasha.

Lokaci na karshe da Aregentina ta kai wasan karshe shi ne a 2014, inda Jamus ta doke ta.

Wannan shi ne karo na shida da Argentina take kai wasan karshe a gasar cin kofin duniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *