“Ina kira ga jami’an tsaro Najeriya da su yi duk abin da za su yi domin ganin an daina kai wa kayayyakin zaben hari”. – Shugaban INEC

Shugaban hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta INEC Farfesa Mahmoud Yakubu ya yi kira ga jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki a kasar, da su yi duk abin da za su yi domin ganin an daina kai wa kayayyakin zaben 2023 hari a ko ina.

Ya yi wannan kira ne lokacin da yake tattaunawa da majalisar wakilai da kuma kwamiin da ya ke bincike kan hare-haren da ake kaiwa kan kayayyakin hukumar.

KARANTA WANNAN LABARI: Buhari ya sake jaddada matsayin gwamnatinsa na ganin an gudanar da tsaftacacen zabe mai inganci a watan fabarairu.

Farfesa Mahmoud Yakubu Ya ce hukumar ta fuskanci hare-hare 50 cikin jihohi 15 a 2019, ya kuma kar da cewa wasu daga cikin jihohin da hare haren su ka faru sun hada da Imo wadda aka kai hari 11, sai Osun da ke da bakwai, sai kuma jihar Enugu da aka kaiwa hare-hare biyar.

Sauran sun hada da Akwa Ibom da ita ma akai kai hari biyar, sai kuma jihohin Cross River da Abiya da dukkansu aka kai hare-hare hurhudu.

Farfesa Mahmoud Yakubu Ya ci gaba da bayyana yadda aka kai hare-hare biyu a jihohin Anambra da Taraba, sai johohin Bayelsa, Ondo, Lagos, Borno, Kaduna da kuma Ogun da dukkansu aka kai musu hari sau daya.

Yayin da kwamitin yake tattaunawa kan yadda za a maye gurbin kayyakin da aka lalata, Farfesa Mahmoud ya bayyana cewa zabe ba zai taba yiwuwa ba a haka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *