Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sake jaddada matsayin gwamnatinsa na ganin an gudanar da tsaftacacen zabe mai ingancin da duniya zata amince da shi a watan Fabarairu, duk da hare haren da batagari suke ci gaba da kaiwa a ofisoshin hukumar zaben kasar.
Buhari ya shaidawa jami’an Cibiyar tabbatar da zaman lafiya dake Washington cewa, har yanzu ya na kan bakansa na ganin an samar da yanayi mai kyau da zai baiwa hukumar zaben damar gudanar da karbabben zabe a shekara mai zuwa.
KARANTA WANNAN LABARIN: “Ina kira ga jami’an tsaro Najeriya da su yi duk abin da za su yi domin ganin an daina kai wa kayayyakin zaben hari”. – INEC
Ko a wannan mako sai da ‘Yan sanda su ka bindige mutane 3 da su ka kai hari Cibiyar hukumar zabe dake Jihar Imo, yayin da hukumar zaben ta kasa ta sanar da cewar a wannan shekara kawai an kaiwa ofisoshinta hare hare har sau 51.
Shugaban Najeriya ya bayyana wadannan hare hare a matsayin tsiraru wadanda ba za su iya shafar kimar zaben baki daya ba, yayin da ya ce an samu ingancin tsaro a wasu yankunan kasar.
A shekara mai zuwa ake saran shugaba Buhari ya kawo karshen wa’adin mulkinsa na shekaru 8, abinda ke nuna cewar Najeriya zata samu sabon shugaban kasa daga cikin ‘yan takarar da su ke ci gaba da karade sassan kasar domin neman goyan baya.
Buhari na ziyara a Amurka ne a karkashin gayyatar shugaba Joe Biden domin halartar taron inganta dimokiradiya, yayin da Biden ya bukaci kasashe 6 na Afrika da zasu gudanar da zabe a shekara mai zuwa da su tabbatar da ganin an yi shi cikin kwanciyar hankali, bayan Amurka tayi alkawarin taimaka musu.