Buhari: “Najeriya ce ta fi dacewa da kasarda masu zuba jari daga Amurka su zuba kudadensu”.

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce Najeriya ce ta fi dacewa da kasardan masu zuba jari daga Amurka su zuba kudadensu.

Shugaban ya bayyana haka ne a a Washington DC yayin da ya ke wata tattaunawa ta musamman ta kasuwanci tsakanin Amurka da Najeriya da kuma zauren masu zuba hannun jari, a wani taro da kungiyar hadinkan.

KARANTA WANNAN LABARIN: A ko ina a duniya dansanda ya na wakiltar al’umma da kuma gwamnati. – Osinbajo

Amurka da Afrika ta shirya tare da hadin gwiwar ma’aikatar kasuwanci da zuba jari, a gefen taron shugabannin Afrika da Amurka.

Muhammadu Buhari Ya ce baya ga yawan da kasar ke da shi, bugu da kari ta na da fadin kasa wanda shi ma wani abun tutiya ne, daga nan ya yi ta zayyano wasu damarmaki da Najeriya ke da su, wanda ya sa ta zama wurin da ya fi dacewa azuba hannun jari.

A cikin wata sanarwa da Malam Garba Shehu mai magana da yawun shugaba Buhari ya fitar, ya ce Nigeria ta na da yawan al’umma ita ce tafi.

Kowacce kasar Afrika karfin tattalin arziki, babu shakka kuma Najeriya ce kan gaba wajen sayen kayayyaki da ake kai wa nahiyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *