“A ko ina a duniya dansanda ya na wakiltar al’umma da kuma gwamnati”. – Osinbajo

Mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya bayyana cewa a ko’ina a duniya dansanda ya na wakiltar al’umma da kuma gwamnati, sannan akwai bukatar a girmama shi.

Osinbajo ya bayyana hakan ne a madadin shugaban kasa lokacin da ya wakilce shi a wurin bayyana rahoton hukumar da ke kula da harkokin ‘yansada na shekara-shekara, karkashin jagorancin makaddashin shugaban hukumar, Clara Ogunbiyi wanda ya jagorancin tawagar zuwa fadar shugaban
kasa da ke Abuja.

KARANTA WANNAN LABARIN: Buhari: Najeriya ce ta fi dacewa da kasarda masu zuba jari daga Amurka su zuba kudadensu.

Hukumar ta gabatar da rahotanta na shekara kamar yadda sashi na 17 da dokokin ‘yansanda ta shekarar 2001 ta tanada.

A cikin sanarwar da mashawarcin mataimakin shugaban kasa, Mista Laolu Akande ya fitar, ya bayyana cewa a kowacce hanya Dansandan Nijeriya aikinsa shi ne tsare al’umma kuma ya na wakiltar mutane ne.

A nasa jawabin, makaddashin shugaban hukumar kula da harkokin ‘yansanda ya ce ko shakka babu gwamnati ta na aiki da tsarin dokar kasa.

Ya ce a matsayin su na hukumar da ke kulawa da harkokin ‘yansanda za su tabbatar da cewa ana amfani da abubuwan da tsarin mulki ya shimfida.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *