“Tun daga shekara ta 2019 zuwa yanzu an kai hari kan ofisoshin hukumar sau 50 a jihohi 15 na kasar”. – INEC

Ya bayyana haka ne a yau Juma’a lokacin da yake bayani ga kwamitin majalisar wakilan Najeriya da ke bincike a kan barnar da aka yi wa INEC.

A cewar Farfesa Yakubu an kai hari sau takwas a shekara ta 2019 a ofisoshin INEC, sau 22 a 2020, sau 12 a 2021 sannan kuma a 2022 an kai hari sau takwas.

KARANTA WANNAN LABARIN: Ƙungiyar dattawan arewa ta nuna damuwa game da zargin cewa wasu ƴan siyasa sun duƙufa wajen sayen katunan zaɓe daga hannun alumma

Shugaban INEC din ya ce an fi kai hare-hare kan ofisoshin hukumar a jihar Imo inda aka kai sau 11 sannan kuma sai jihar Osun inda aka kai hari sau bakwai.

Galibin hare-haren an kaddamar da su ne a jihohin da ke kudancin Najeriya. Farfesa Yakubu ya ce duk da irin wadannan matsalolin, suna ci gaba da gudanar da shirye-shiryen da suka kamata domin tsara zabe mai inganci a Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *