Ganduje: “Takardun sa hannun hukuncin a rataye Abduljabbar Nasir Kabara nake jira”.

Gwamnan Jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, yace takardunsa hannun hukuncin a
rataye Fitaccen malamin addinin musuluncin nan Abduljabbar Nasir Kabara yake jira.

Wata kotun musulunci ce da ke zamanta anan Kano ta zartar da hukuncin kan zargin Malamin da batanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad SAW.

Da sanyin safiyar jiya ne aka gurfanar da Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara a gaban kotun Kofar Kudu da ke birnin Kano.

KARANTA WANNAN LABARIN: Babban Sufeton ‘yan sandan kasarnan ya gargadi dukkanin masu kai farmaki ga ofisoshin INEC

Tun da farko Mai shari’a Ustaz Ibrahim Sarki Yola, ya ce ya gamsu da shaida da hujojjin da aka gabatar masa game da karar da ake yi wa Abduljabbar na yin batanci ga Annabi Muhammad S.A.W.

Ya ce hujojji sun bayyana cewar Abduljabbar ne ya kirkiro dukkanin wadannan kalamai a cikin karatunsa.

Adon haka kotun ta same shi da laifin da ake tuhumarsa dashi da aikatawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *