Babban Sufeton ‘yan sandan kasarnan ya gargadi dukkanin masu kai farmaki ga ofisoshin INEC

Babban Sufeton ‘yan sandan kasarnan, Usman Alkali Baba ya gargadi dukkanin masu kai farmaki ga ofisoshin hukumar zabe ta kasa (INEC) a sassan kasar nan da cewar rundunar ‘yan sanda ba zata taba lamuntar hakan ba kuma za su dakile duk wani harin da ake shirin kaiwa ofisoshin hukumar INEC.

Sufetan ‘yan sandan ya kuma sake nanata yunkurin rundunar tare da yin hadaka da sauran hukumomin tsaro wajen tabbatar da sahihi kuma ingattaccen zabe a 2023 kamar yadda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi alkawari.

KARANTA WANNAN LABARIN: Ganduje: “Takardun sa hannun hukuncin a rataye Abduljabbar Nasir Kabara nake jira”.

Baba ya shaida hakan ne a yayin ganawa da manyan jami’an ‘yan sanda da suka kunshi kwamishinonin ‘yan sanda dangane da batun zaben 2023 da ya gudana a shalkwatar rundunar da ke Abuja.

Ya kuma ce, ‘yan sanda sun fito da sabbin dabarun aiki bisa kwarewa wajen shawo kan matsalolin da ka iya tasowa a lokacin zaben 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *