Akwai fursononi 3,167 aka yanke wa hukuncin kisa a Najeriya. – NCoS

Hukumar da ke kula da gidajen yari ta Najeriya (NCoS) ta bayyana cewa an yanke hukuncin kisa ga akalla fursunoni 3,167 da ke zaman cibiyoyin gyaran hali daban-daban a kasar nan.

Kakakin NCoS, Abubakar Umar wanda ya bayyana hakan a wani taron manema labarai ranar Alhamis a Abuja.

Ya ce wannan 3,167 na daga cikin fursunoni 74,824 da ke tsare a gidajen yarin Najeriya a fadin kasar nan a wani bincike da aka yi a ranar 12 ga watan Disamba, 2022.

Umar ya kuma bayyana cewa jimillar fursunoni 52,178 ne ke jiran shari’a daga cikinsu maza 50,955 yayin da mata 1223 ke jiran shari’a.

A da dama daga cikin wadanda aka yankewa hukuncin, Umar ya bayyana cewa fursunoni 19,479 da ake tsare da su ne kawai aka yanke musu hukunci, inda ya ce a cikin wannan adadi, 19,140 maza ne yayin da sauran 339 mata ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *