Ƙungiyar tace sayar da katin zaɓen yana da hatsari sosai, sakamakon yadda zai iya cutar
da yankin.
Dr Hakeem Baba Ahmed shi ne kakakin ƙungiyar kuma ya shaida cewar sun daɗe da samun labarin yadda ake zagayawa ana karɓar katunan zaɓen jama’a musamman mata.
KARANTA WANNAN LABARIN: “Tun daga shekara ta 2019 zuwa yanzu an kai hari kan ofisoshin hukumar sau 50 a jihohi 15 na kasar”. – INEC
Ya ce masu yin wannan abu na bijiro da wata dabara ta shawo kan mutane suba da katinsu da sunan taimaka musu wajen shiga wani shirin yaƙi da talauci.
A cewarsa, wannan dabara ta ƙwacewa mutane katin zaɓensu na faruwa a kowacce jam’iyya ba wai wata jam’iyya ɗaya ba.
Ƙungiyar dattawan arewan ta yi kira ga hukumomi dasu ƙara kaimi wajen magance
matsalar tun kafin lokacin zaɓen