Da Ɗuminsa: Kotu ta yanke wa Sheikh Abduljabbar hukuncin kisa ta hanyar rataya

Da Ɗuminsa: Kotu ta yanke wa Sheikh Abduljabbar hukuncin Kisa ta hanyar rataya

Kotu ta yanke wa Sheikh Abduljabbar Hukuncin kisa ta hanyar rataya sakamakon ɓatanci da ya yiwa Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama.

Mai sharia Ustaz Ibrahim Sarki Yola na kotun Musulunci a Jihar Kano, ya ce kotu ta tabbatar da cewar kalaman batanci da Abduljabbar ya yi ga Ma’aiki SAW a cikin karatun sa, shine ya kirkire su da kansa domin shaidu da hujjojin kotu sun tabbatar da cewa babu su a cikin litattafan da yake fada.

A saboda haka aka yanke mashi hukuncin kisa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *