Majalissar Wakilai Ta Baiwa NNPC Mako 1 Domin Kawo Karshen Karancin Man Fetur A Kasar

Majalisar wakilai ta umarci kamfanin man fetur na kasa (NNPC) Limited da sauran hukumomin da ke kula da harkokin man fetur da su kawo karshen matsalar karancin man fetur a cikin mako guda domin rage radadin da ‘yan Najeriya ke ciki.

Rahma ta rawaito cewa, Umurnin ya biyo bayan amincewa da kudirin da Sa’idu Musa Abdullahi na jam’iyyar APC, daga jijar Neja ya gabatar a zauren majalisar a ranar Talata.

Da yake gabatar da kudirin, ya ce a cikin ‘yan watannin da suka gabata ‘yan Nijeriya sun fuskanci wahalhalun da ba za a iya mantawa da su ba sakamakon karancin man fetur da ake fama da shi, lamarin da ya yi illa ga harkokin tattalin arziki wanda a yanzu wahalar kasar nan ta fi tsanani.

Ya ce Hukumar Kula da Man Fetur ta Najeriya (NMDPRA) ta gabatar da uzuri da dama saboda karancin mai.

Dan majalisar ya bayyana cewa, “Da farko, a lokacin da karancin man fetur ya taso a daidai lokacin damina a watan Oktoban bana, NMDPRA ta ce karancin man fetur da ake fama da shi a Abuja da sauran jihohin Arewa ya samo asali ne sakamakon ruwan sama da ya mamaye babbar hanyar Lokoja ciki har da babbar hanyar da za ka bi Abuja, ci gaban da ya hana duk wani motsin ababen hawa a wannan hanyar.

“Ba da jimawa ba bayan ambaliya ruwan sama da aka yi a Lokoja kuma aka ci gaba da fama da karancin man fetur, Shugaban kungiyar dillalan man fetur ta kasa IPMAN ya ce lamarin ya ci gaba da wanzuwa saboda gibin samar da kayayyaki da aka yi a Lokoja.

Kungiyar ta IPMAN ta tabbatar da cewa akwai isassun kayayyaki a cikin ma’ajiyar, kuma karancin kayan da ake samu ya faru ne kawai saboda karayawar da aka samu wajen dakon man.

Lokacin da aka ci gaba da samun karanci kuma duk uzurin da masu ruwa da tsaki suka yi ya kawo cikas, sai hukumar kula da ayyukan IPMAN ta kasa ta kara da wani dalili kuma ta ce karancin ya faru ne saboda rashin wadatar kayayyakin.

“Rahotanni na sirri kan karancin man fetur da jami’an tsaronmu suka tattaro a halin yanzu sun nuna cewa akwai wani shiri da wasu ‘yan kasuwar man fetur suka shirya na dakile yunkurin gwamnati na rarraba man fetur a kasar nan ta hanyar tara man fetur din, wanda hakan ya haifar da karancin man fetur a ko’ina a kasar“.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *