Hukumar tsaron farin kaya ta DSS, ta Gayyaci Masu Kasuwar Man Fetur Na Nijeriya (IPMAN) , da hukumar kula da harkokin man fetur da sauran masu ruwa da tsaki, inda ta umurci su da su gaggauta magance matsalar karancin man.
A cewar wani babban jami’in DSS, wanda bai so a ambaci sunansa ba, an yi shi ne a ranar Litinin da ta gabata, inda aka kwashe sa’o’i da dama a tsakanin jami’an tsaro, ‘yan kasuwar man fetur da sauran masu ruwa da tsaki.
Ya ce, dilalan a taron, sun bayyana wa hukumar DSS matsalolin da suke fuskanta da kuma yadda za a kai kayayyaki daga sassan Najeriya zuwa Kano.
A cewarsa, wasu daga cikin kalubalen da suke fuskanta sun hada da tsadar shigo da man fetur ga wannan bangare na al’ummar kasar, rashin kyawawan hanyoyi da ke haifar da lalacewar tayoyinsu akai-akai, da kin biyansu kudaden Sufuri.
Hakazalika, Ma’aikatar Albarkatun Man Fetur, DPR, ta riga ta kafa wata tawaga ta mutum uku da za ta sanya ido a kai a Kano, wadda za ta fara aiki, a ranar Talata domin tabbatar da wadatar da jama’ar Kano ba tare da katsewa ba.
Hukumar ta DPR, ta ce ta baiwa hukumar DSS tabbacin tabbatar da bin ka’idar samar da mai ba tare da katsewa ba wanda nan da ‘yan kwanaki masu zuwa za ta kubutar da Kano daga dogayen layukan masu ababen hawa a gidajen man.