Qatar 2022: Morocco Ta Kafa Tarihi A Gasar Cin Kofin Duniya 

Tawagar kwallon kafar Morocco ta kafa tarihin zama kasar Afirka ta farko  da ta samu damar zuwa wasan kusa da na karshe na gasar cin kofin duniya, sakamakon nasarar da kasar ta samu akan Portugal da ci 1-0 a gasar dake gudana a kasar Qatar. 

Dan wasan gaba Youssef En-Nesryi ya jefa wa Morocco kwallon ta guda daya tilo a minti 42 na wasan, wanda mai horar da yan wasan Portugal ya sake ajiye Cristiano Ronaldo a benci har zuwa bayan hutun rabin lokaci. 

A wani labari kuma: Farashin doya ya sauka a kasuwanin jihar Neja.

Wannan nasara ta Morocco ta zarce na duk wata kasar Afirka a gasar cin kofin duniya, musamman na Kamaru da Senegal da suka samu damar zuwa matakin kwata-final a shekarar 1990 da 2002, sai kuma Ghana a gasar shekarar 2010. 

Yanzu Morocco zata jira wanda zai samu nasarar a karawar da za’ayi daren yau tsakanin Faransa da Ingila domin karawar da za suyi ranar laraba a wasan kusa da na karshe, yayin da Argentina zata kara da Croatia. 

Yayin karawar ta yau, Cristiano Ronaldo ya kafa wani tarihi na buga wasanni 196 a gasar cin kofin duniya, tarihin da Bader Al-Mutawa, dan kasar Kuwait ke rike da shi. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *