Farashin doya ya sauka a kasuwanin jihar Neja.

Farashin doya ya sauka a jihar Neja yayin da manoma suka fara cika kasuwanni.

Binciken da aka yi a manyan kasuwannin doya da suka hada da na Paiko hedikwatar karamar hukumar Paikoro da kuma kasuwannin Gwari da Gwadabe da ke Minna babban birnin jihar ya nuna cewa farashin kayan ya ragu da sama da kashi 30 cikin dari.

Daya daga cikin manoma kuma mai sayarwa a kasuwar Paiko, Mohammed Salihu, ya shaida wa wakilinmu cewa, doya 100 na irin dawa da aka fi sani da kwariya a kasar Hausa, wanda ake sayar da shi Naira 200,000 kafin zuwan sabon dawa, yanzu ana sayar da shi akan N40. 000 da N70,000, gwargwadon girmansu.

A wani labari kuma: Qatar 2022: Morocco Ta Kafa Tarihi A Gasar Cin Kofin Duniya 

Ya ce yawanci manoman ba su fito da sabuwar doyar ba saboda har yanzu suna jin daɗin ribar da suka samu wajen sayar da waken soya daga girbin da aka kammala, suna fatan masu saye za su ji dadin sabon farashin kafin daga watan Janairu lokacin da za a fara shirye-shiryen sabuwar kakar noman.

Manoman sun ce duk da kalubalen tsaro da ya addabi manyan al’ummomin da suke noman doya a kananan hukumomin Munya, Paikoro, Shiroro, Rafi da sauran su, manoma sun samu girbi mai kyau a bana.

Binciken mu da muka yi ranar Lahadin da ta gabata ya kuma nuna cewa, hijirar dimbin manoman Gbagyi daga kananan hukumomin Shiroro da Munya da Rafi da Paikoro da jami’an tsaro suka yi kaka-gida a daminar da ta wuce zuwa yankunan Nupe a yankin Neja ta Kudu, inda akwai filaye masu albarka na noma shine ya haifar da girbi mai yawa.

Wani wanda ya zo siyan doya a kasuwar, Mohammed Musa, ya kuma tabbatar wa Rahma a ranar Lahadi a kasuwar Gwadabe da ke Minna cewa ya sayi bututun doya guda 10 a kan Naira 3,500, inda ya ce, “Da a da, da ya kai ku tsakanin N8,000 zuwa N9,000. A gaskiya farashin doya ya sauko.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *