Zainab Shamsuna: Gwamnatin tarayya za ta sake duba ka’idojin da bankunan raya kasa

Ministar kudi, kasafi da tsare-tsare ta kasa, Zainab Shamsuna Ahmed, ta ce gwamnatin tarayya za ta sake duba ka’idojin da bankunan raya kasa da ake amfani da su wajen bayar da lamuni ga masu kananan sana’o’i da matsakaitan masana’antu a kasar nan domin tabbatar da yaduwar rage talauci a fadin kasar nan.

Zainab Ahmed ta bayyana haka ne a ranar Alhamis a lokacin da ta bayyana a gaban kwamitin wucin gadi na Majalisar Dattawa da aka kafa domin gudanar da bincike a kan zargin karkatar da kudaden bashin Naira biliyan 500 na Gwamnatin Tarayya da bankunan ci gaba.

Idan dai za a iya tunawa, Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan, bayan
wani kudiri da Sanata Ali Ndume ya gabatar, ya kafa wani kwamitin da
Sanata Sani Musa ya jagoranta domin gudanar da bincike kan lamarin.
Ndume ya yi ikirarin cewa shiyyar Kudu-maso-Yamma a yankin siyasar
kasar nan, musamman jihar Legas ce ta fi yawan wadanda suka ci gajiyar
rance a kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *