Wani kwamiti na musamman da shugaban kasa ya kafa domin ya gudunar da bincike a kan cajin cirewa da ajiyar kudi a asusun banki ya yi zargin cewa wasu hukumomin da binciken ya shafa suna kokarin hana shi yin aikin sa, da kuma hana shi ya mika wa shugaba Buhari rahotonsa.
Kwamitin wanda aka dora masa alhakin binciken cajin kudin ajiya da cire kudin tun daga shekara ta 2013 zuwa yanzu ya gano cewa babban bankin kasar ya tara fiye da naira tiriliyon tamanin, amma ya yi zargin cewa ana sama da fadi da kudin.
A wani labarin kuma:
Muhammad Gudaji Kazaure, shi ne sakataren kwamitin yace sun gano wasu makudan kudade.
Ya ce akwai naira miliyan dubu dari da 71 na cikin asususn ajiya na farko zuwa shekarar 2020, kuma akwai bashin naira tiriliyan 23.4 da aka ba bankuna.