Shugaban NERC: “Mun rusa gine-gine kusan 5,000 da ke ƙarƙashin manyan wayoyin lantarki a faɗin ƙasar nan”.

Shugaban hukumar kula da harkokin wutar lantarki ta kasa ya ce sun rusa gine-gine kusan 5,000 da ke ƙarƙashin manyan wayoyin lantarki a faɗin ƙasar nan Aliyu Tahir wanda shi ne kuma babban jami’in lantarki na ƙasa.

Yace tun 2017 aka ɗauki mataki tare da ba da umarnin rushe gine-ginen da ke ƙarƙashin wayoyin, kamar yadda kamfanin labarai na NAN ya ruwaito.

NEMSA ta ce akwai buƙatar gaggauta katse yankunan daga layin lantarki da kuma rushe su daga baya.
Ya Kara dacewa sun bai wa kamfanonin rarraba lantarki umarnin sauke duk wani gini da aka yi a ƙarƙashin babban layin lantarki daga kan layin wutar, har ma da waɗanda suka tare hanya.

Tahir ya ƙara da cewa rushe gine-ginen na buƙatar himma daga waɗanda abin ya shafa.

Ko anan jihar Kano a farkon makon Nan wadanda suke zaune a karkashin babbar wayar ta lantarki suka Gudanar da sallolin Nafila da aduoi Dan samun mafita akan halin da suke ciki na barazanar tashinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *