Muhammadu Buhari ya bukaci da a gaggauta kaddamar da matakai kan yaki da ta’addanci a yankin yammacin Afirka.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi a wurin taron shugabannin ECOWAS karo na 62 wanda ya gudana a Abuja.

Ya kara da cewa akwai bukatar sauya salon yaki da ‘yan ta’adda a yankin yammacin Afirka.

A cewarsa, wannan yunkuri zai karfafa kokarin gwamnatocin yanki wajen tabbatar da ci gaba mai dorewa a yammacin Afirka.

Ya yi kira ga sabon tawagar ECOWAS wanda Dakta Omar Alieu Toure yake jagoranta kan gaggauta kammala nazari na sake fasalin kungiyar domin samun inganta yankin yammacin Afirka.

Da yake yi wa shugabannin yankin maraba, Buhari ya ce taron wannan shekarar shi ne na 8 da Nijeriya ke shiryawa.

Shugaban Buhari ya jinjina wa takwaransa na kasar Ghana, Nana Akufo Addo wanda ya kasance tsohon shugaban kungiyar bisa shugabancinsa.

Buhari ya godewa shugabannin bisa goyon bayan da suka bayar wajen rawar da suka taka lokacin annobar Korona kan hadin kai yankunan yammacin Afirka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *