FG: “Sama da mutune miliyan shida ne sauyin yanayi ya ɗaiɗaita a Najeriya tsakanin shekara ta 2008 zuwa 2021”.

Gwamnatin tarayya ta ce sama da mutune miliyan shida ne sauyin yanayi ya ɗaiɗaita a Najeriya tsakanin shekara ta 2008 zuwa 2021.

Babban kwamishina a hukumar kula da ‘yan gudun hijira da ‘yan cirani , Imam Sulaiman-Ibrahim ne ya bayyana hakan a tattaunawarsa game da yawan hijira da aka gudanar a Abuja.

Ya bayyana cewa rahoton hukumar sa ido kan ‘yan gudun hijira, ya nuna cewa ƙasar ta fuskanci bala’o’i na sauyin yanayi 131 a tsawon wannan lokaci.

Ya kara da cewa alkaluman sun fi na yawan mutane miliyan 4 da rabi da rikice-rikice ya ɗaiɗaita. Tun da farko a jawabinta, ministar ma’aikatar agaji Sadiya Umar-Faruk, ta ce gwamnatin tarayya, ta nuna jajircewarta wajen takaita bala’o’in da sauyin yanayi ya haddasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *