Shugaban marasa rinjaye na majalisar Phillip Aduda ya janyo hankalin wakilan majalisar kan cewa matakin na CBN zai yi illa ga al’umma musamman ma masu ƙananan sana’o’i.
A nasa tsokacin, shugaban majalisar sanata Ahmed Lawan ya ja hankalin bankin na CBN da ya yi nazari kan lamarin kafin yanke hukunci kai-tsaye, kasancewar matakin zai shafi mutane da dama.
Ya kuma ce akwai bukatar a tattauna da bankin domin samun cikakken bayani kan tsarin, sannan ya bukaci kwamitin kula da harkar bankuna na majalisar ya tattauna kan batun a lokacin zaman tantance mataimakan shugaban bankin, wanda ake sa ran yi a mako mai zuwa.
A karkashin sabon tsarin na CBN, ɗaiɗaikun mutane na da damar cire naira 100,000 ne kacal a mako, yayin da kamfanoni za su iya cire naira 500,000 a mako.
A kan wannan dai Majalisar dattawan ta yi sammacin wasu mataimakan gwamnoni biyu na babban bankin Najeriya da su bayyana gabanta a gobe Juma’a domin yin cikakken bayani kan dokar takaita fitar da kudade da babban bankin ya bayyana a ranar Talatar da ta gabata.