Babban Hafsan Tsaro Na Najeriya, Janar Lucky Irabo, ya ce rundunar soja na fuskantar matsin lamba don yin katsalandan a babban zaben shekarar 2023.
Shugaban sojan, amma ya ce rundunar sojojin za ta cigaba da aikinta ba tare da nuna bangaranci ba kuma za ta taimakawa rundunar yan sanda don sa ido tare da bada tsaro don zabe.
Irabor ya yi magana ne a ranar Alhamis yayin taron manema labarai da tawagar sadarwa ta shugaban kasa ta shirya a fadar villa da ke Abuja.
Shugaban tsaron ya tabbatar da cewa sojojin ba yan siyasa bane, yana mai cewa ana saka matakai da suka dace don tabbatar an bi umurnin Shugaba Muhammadu Buhari na rashin nuna bangaranci.
Ya ce an bawa jami’an sojojin horaswa na yin aiki a matsayin kwararru sannan an sanar da su dokokin aiki kafin, yayin da bayan zabe.
Irabor ya kara da cewa kuma ana bawa jami’ai da dakarun sojojin horaswa ta musamman kan ayyukan zabe.