Shugaba Vladimir Putin ya ce rabin ‘yan kasar Rasha da aka kira zuwa aikin soja a watan Satumba an tura su zuwa Ukraine. Shugaban ya ce daga cikin sojoji 300,000 da aka dauka aiki, an tura 150,000 fagen daga.
Mista Putin wanda ya bayyana hakan yayin wata ganawa da kwamitinsa da ke kare hakkin bil’adama, wanda aka nuna a gidan talibijin din kasar, ya ce yanzu haka 77,000 daga cikin sojoji na
cikin shirin ko ta kwana.

Rashad ai ta zargi Majalisar Dinkin Duniya da sauran kungiyoyin kasa da kasa da kuma kafafen yada labaran yammacin duniya da kokarin bata mata suna.
Ya kuma zargi kafofin yada labaran kasashen waje da yada “labaran karya” game da yakin da Moscow na soja ke yi a Ukraine.
Shugaba Vladimir Putin wanda ya sha alwashin yin amfani da dukkan hanyoyin soji wajen kare kasar Rasha, Moscow za ta yi amfani da makaman nukiliya a matsayin martani ga harin da
abokan gaba suka kai musu.