FG: “Za a bude gadar Neja ta biyu don zirga-zirga daga ranar 15 ga watan nan na Disamba”.

Kwanturolan ayyuka na gwamnatin tarayya a jihar Delta, Mista Jimoh Olawale, ya ce za a bude gadar Neja ta biyu don zirga-zirga daga ranar 15 ga watan nan na Disamba.

Olawale, wanda ya bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya a Asaba, ya ce za a bude gadar ne na tsawon kwanaki 30 kacal.

Ya yi nuni da cewa, Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola, ya bayar da umarnin bude gadar wadda aka kammala kashi 95 cikin 100 na aikinta, domin saukaka zirga-zirga a lokacin bukukuwan kirsimati da na sabuwar shekara.

Sai dai Olawale ya karyata ikirarin da wata kungiya ta yi na cewa Gwamnatin Tarayya ta yi watsi da biyan diyya ga masu kadarorin da ke kan hanyar shiga gadar Neja ta biyu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *