“Rashin tabbas game da samun kulawa bayan yin ritaya ne ke rura wutar ayyukan rashawa tsakanin ma’aikatan gwamnatin ƙasar”. – Jonathan

Jonathan ya bayyana haka ne a ranar Talata a lokacin ƙaddamar da wani littafi game da rayuwar tsohon limamin cocin fadar gwamnatin tarayya, Obioma Onwuzurumba.

A cewar tsohon shugaban ƙasar “ɗaya daga cikin manyan matsalolin Najeriya, wanda ga dukkan alamu shine yasa rashawa yayi katutu.


Inda ya ƙara da cewar doka bata baiwa ma’aikata damar yin kasuwanci ko mallakar kamfanoni ba, sannan babu wanda zai kula da kai ko yaranka bayan ka bar aiki.

Daga nan sai ya buƙaci masu hali su samar da wani shiri na tallafa wa tsofaffi, domin a cewarsa hakan zai taimaka wajen rage matsalar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *