NAFDAC: “Zamu kawar da kasuwanni da shaguna da masu shigo da man bilicin wanda ba’a amince da shi ba”.

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) ta ce zata kawar da kasuwanni da shaguna da masu shigo da man bilicin wanda ba’a amince da shi ba.

Hukumar ta ce za ta fara aiwatar da aikin ne a shagunan kayan kwalliya da kuma shagunan da ake sarrafa irin mayukan wanda basu samu sahalewar hukumar ba.

Hukumar na bayyana wannan batun ne a wani taron bita da hukumar ta shirya, tare da hadin gwiwar kungiyar ‘yan jaridun lafiya ta Najeriya.

Mukadashin daraktan ta hukumar tace akwai wadanda ake hadawa a gida, ana amfani neda sinadaran da ake shigowa da su wanda hukumar ta amince musu, amma kuma sai a sarrafasu yadda bai kamata ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *