Kotun kolin kasarnan tayi watsi da jita-jita cewar hukumar tsaro ta DSS ta gurfanar da Mai shari’a Olukayode Ariwoola.

Kotun kolin kasarnan tayi watsi da wata jita-jita cewar hukumar tsaro ta DSS ta gurfanar da babban jojin Najeriya Mai shari’a Olukayode Ariwoola bisa zarginsa da furta kalaman siyasa

Kotun kolin kasarnan tayi watsi da wata jita-jita cewar hukumar tsaro ta DSS ta gurfanar da babban jojin Najeriya Mai shari’a Olukayode Ariwoola bisa zarginsa da kalaman siyasa na goyon bayan Wike.

Kotun kolin ta kuma yi watsi da ikirarin na cewar alkalai biyar na kotun sun bukaci babban jojin da ya yi murabus daga mukaminsa a kan wannan batu.

A wata sanarwa da Daraktan yada labarai na kotun, Dr Festus Akande, ya fitar, yace kotun kolin ta gargadi masu yada jita-jitar da su daina domin biyan bukatun kansu.

Kotun kolin ta kuma mayar da martanin ne kan wani labari da wata kafar yada labarai ta intanet ta wallafa, inda ta ce hukumar DSS ta gurfanar da Mai shari’a Ariwoola bisa zarginsa da furucin siyasa a Fatakwal a wani taron jama’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *