Gwamnatin tarayya ta kafa kwamiti da zai gudanar da bincike a kan zarge zargen satar man da ake yi.

Gwamnatin tarayya ta kafa wani babban kwamiti mai mutane 11 da zai gudanar da bincike a kan zarge zargen satar man da ake yi wa wasu shafaffu da mai da kuma jami’an tsaro, abin da ke sanya kasarnan kasa fitar da man da take bukata da kuma sanya ta asarar makudan kudade.

Mai bai wa shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro Janar Babagana Monguno ne ya kaddamar da kwamitin, wanda ke karkashin tsohon janar na sojin Najeriya, Barry Ndiomu, yayin da David Attah zai zama Sakatare.

Monguno ya ce abin takaici ne ganin yadda Najeriya ke tafka asarar makudan kudade saboda yadda wadannan barayin mai suka yi karfi, suke kuma cin amanar kasa wajen sace danyen man da kasar ta dogara da shi wajen samun kudaden shiga daga kasashen ketare.

Ya danganta satar man da yaddda kasar take asarar kudaden shigar da ta saba samu, wadanda ake gudanar da ayyukan raya kasa da su.

Monguno ya ce abin takaici ne yadda a halin yanzu Najeriya ke shan wahala wajen samar da ganga miliyan guda kowaccce rana, sabanin ganga miliyan guda da dubu 800 da kungiyar kasashe masu arzikin mai na OPEC ta bata damar fitarwa.

Ya kara da cewar ya zama wajibi a gudanar da binciken domin gano masu hannu a ciki da wadanda ake hada baki da su, ciki harda jami’an tsaro da kamfanonin kasashen ketare domin daukar mataki mai tsauri a kai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *