Hukumar kula da yanayi ta kasa ta yi hasashen cewar nan da kwana ɗaya hazo zai lulluɓe wasu jihohin arewacin ƙasarnan sanadiyyar iska da za ta kwaso ƙura daga ƙasashe maƙwaftaka.
Wata sanarwa da hukumar ta fitar ta hannun jami’inta na hulɗa da jama’a, Muntari Yusuf, ta ce yanayin zai yi ƙamari na tsawon kwana uku.
Ta ƙara da cewa bayanan da aka samu bayan lura da yanayi a jamhuriyar Nijar, da Chadi sun nuna yadda iska mai ƙarfi za ta kwaso ƙura har zuwa yankin arewa-maso-tsakiyar Najeriya.
Jihohin da lamarin zai fi ƙamari a cewar sanarwar su ne Katsina, da Zamfara, da Kano, da Kaduna, da Yobe da kuma Jigawa.
Ana kuma sa ran cewar yanayin zafi zai sassauto.
Hukumar ta buƙaci al’ummar jihohin da lamarin zai shafa su ɗauki matakan kariya domin ƙurar da za ta iya cutar da lafiya.
Ta kuma akwai buƙatar a tanadi kayan sanyi musamman ga yara saboda
yanayin sanyi da za a fuskanta.