PDP Ta Naɗa Dogara a Cikin Kwamitin Yakin Neman Zaben Atiku

Jam’iyyar PDP Ta Naɗa Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai Kuma Babban Jigon APC, Yakubu Dogara a Cikin Kwamitin Yakin Neman Zaben Atiku.

Kwamitin yakin neman zaben (PCC) a ranar Lahadi ta sanar da tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, a matsayin mamba na kwamitin.

Babban Darakta na kwamitin jam’iyyar PDP a yakin neman zabe PCC, Aminu Tambuwal, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, ya ce nadin Dogara “yana daga cikin ayyukan da muke ci gaba da yi na hada kai da dan takararmu na shugaban kasa, Atiku Abubakar, domin mu maido da martabar babbar kasar mu Najeriya”.

Mun ta tattaro cewa, Dogara ya jagoranci gungun ‘ya’yan jam’iyyar APC arewa wajen daukar Atiku a matsayin dan takarar shugaban kasa a zaben 2023.

Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Bogoro da Dass da Tafawa Balewa na tarayya ya yi Allah wadai da tikitin mabiya dan takarar APC Bola Tinubu da Kashim Shettima.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *