An daɗe ba a samu irin wannan rikicin ba a yankin da lamarin ya faru amma Shugaba Feliz Tshisekedi ya bayyana cewa sama da mutum ɗari ne aka kashe a ƙauyen Kishi-she.
Gwamnatin ƙasar ta ɗora alhakin kisan kan ƴan tawayen M23, duk da cewa sun musanta zargin.
An ta samun ƙarin rikice-rikice tun bayan da Jamhuriyyar Congo da Rwanda suka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a makon da ya gabata.
Congo da Amurka da Majalisar Ɗinkin Duniya duk sun zargi Rwanda da goyon bayan yan tawayen M23 duk da cewa Rwandan ta musanta hakan.