Iran ta rushe Rundunar Hisbah ta ƙasar.

Babban lauyan gwamnatin Iran, Mohammad Jafar Montazeri ya ce hukumomi sun rushe rundunar ‘yan Hisbah ta kasar.

Zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, sauran kamfanonin dillancin labarai ba su tabbatar da kalaman nasa ba, waɗanda aka ce ya yi ne a wani wurin taro ranar Lahadi.

An samar da jami’an ne domin tabbatar da bin tsarin sanya tufafi na Musulunci.

“‘Dakarun Hisbah ba su da wata alaƙa da ma’aikatar shari’a kuma an soke su daga inda aka kafa su,” a cewarsa.

Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Iran ce ke kula da ayyukan dakarun, ba ma’aikatar shari’a ba.

A ranar Asabar, Mista Montazeri ya faɗa wa majalisar ƙasar cewa za a sake duba dokar da ta tilasta wa mata saka hijabi.

Kasar Iran na fama da mummunar tarzomr ƙin jinin gwamnati tun bayan da wata matashiya mai shekara 22, Mahsa Amini ta rasu a hannun ‘yan sanda.

An kama ta ne bisa zargin ƙin ɗaura dan kwalinta ko hijabi yadda ya kamata.

Idan batun ya tabbata, rusa rundunar kamar shan kaye ne a wajen gwamnati amma babu tabbas ko hakan zai sa masu zanga-zangar su daina fitowa.

“Kawai don gwamnati ta rusa ‘yan Hisban hakan ba ya nufin zanga-zangar ta zo ƙarshe,” kamar yadda wata ‘yar Iran ta faɗa wa BBC.

“Hatta abin da gwamnatin ke faɗa cewa saka hijabi ba wajibi ba ne bai ishe mu ba. Mutane na sane cewa Iran ba ta a tabbas a ƙarƙashin wannan gwamnatin,” in ji ta.

Tun a shekarar 1983 ne aka yi dokar tilasta wa mata sanya hijabi a kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *