Gwamnonin jihohin Najeriya 36 sun ce sun yi mamakin yadda ƙaramin Ministan Kasafin Kuɗi da Tsare-Tsare na ƙasar, Clem Agba ya zarge su da jefa Najeriya cikin talauci.
A watan Nuwamba ne Hukumar ƙididdiga ta Najeriya ta ce mutum miliyan 130 ne a ƙasar ke fama da talauci, kusan kashi 63 cikin 100 na a’umar ƙasar.
To sai dai a wata sanarwa da ƙungiyar gwamnonin ƙasar suka fitar mai ɗauke da sa hannun daraktan yaɗa labaran ƙungiyar Abdulrazaque Bello- Barkindo, ta bayyana kalaman ministan da cewa abu ne da bai kamata ba, kuma babu kanshin gaskiya a cikin kalaman ministan.
Gwamnonin sun ce iƙirarin – da ministan ya yi cewa gwamnonin sun yi watsi da al’ummar karkara – ba shi da tushe balle makama.
A cikin makon da ya gabata ne dai ƙaramin ministan Kasafin Kuɗi da Tsare- Tsare Clem Agba a wani taro da ya yi da manema labarai bayan taron majalisar zartarwa ya ɗora alhakin katutun talaucin da ke damun ƙasar nan.
gwamnonin jihohi.
majalisar zartarwa ya ɗora alhakin katutun talaucin da ke damun ƙasar kan
gwamnonin jihohi.