A wata sanarwa da hukumar ta wallafa shafinta na Tuwita ta ce ta saka ranar Litinin 12 ga watan Disamba zuwa Lahadi 22 ga watan Janairun 2023 a matsayin ranakun da za ta rabar da katinan zaɓen a ofisoshinta da ke faɗin ƙananan hukumomin ƙasar 774.
Tuni dai hukumar ta sanar da ranar 25 ga watan Fabrairun 2023 a matsayin ranar da za ta gudanar da zaɓen shugaban ƙasar tare da na ‘yan majalisun dokoki.
Yayin da za a gudanar da zaɓen gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi ranar 11 ga watan Maris ɗin 2023.