A wata sanarwar haɗin gwiwwa da ƙungiyoyin NLC da TUC suka fitar, sun ce ba su ga dalilin da zai sa a samu ƙarancin fan a fadin ƙasar ba, saboda a cewarsu gwamnati ce kaɗai ke da alhakin shigo da man cikin ƙasar.

Dan haka a cewarsu ba su ga dalilin da zai sa wata hukuma ta gwamnati za ta ƙara kuɗin da take sayar wa ‘yan kasuwa ba.
Sanarwar ta ƙara da cewa ƙungiyoyin sun samu wata masaniya da ke nuna cewa da gayya aka ƙirƙiri matsalar domin a riƙa sayar da man sama da farashin da gwamnati ta amince da shi.
Kungiyoyin ƙwadagon sun umarci gwamnati da ta gaggauta kawo ƙarshen matsalar kafin abubuwa su lalace.