Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Usman Baba Ya Bukaci Kotu Ta Soke Hukuncin Da Ta Yi Masa Na Daurin Watanni Uku

Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Usman Baba, ya ce ya garzaya wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, inda ya shigar da bukatar a yi watsi da shari’ar rashin gaskiya da kuma hukunta shi.

A cikin karar da aka shigar a ranar Alhamis, Baba ya yi karin haske kan dalilan da ya sa ya kamata a yi watsi da umarnin.

Ya ce ya samu shawarar da ta dace ta fannin shari’a daga kwamishinan ‘yan sandan da ke kula da sashin shari’a na rundunar.

Kakakin rundunar, Olumuyiwa Adejobi, a wata sanarwa da ya fitar da safiyar Juma’a, ya ce babban dan sandan ya bayyana cewa ba a nada shi mukamin IGP ba a lokacin da aka fara shari’ar kuma aka amince da sake dawo da shi bakin aiki.

Ya kuma kara da cewa, an gudanar da shari’ar cin mutuncin ne ta hanyar canza sheka a watan Nuwambar shekarar  2018 da Janairun shekarar 2019, a kan Sufeto-Janar na ‘yan sanda na lokacin, ba wai a matsayinsa na mai ci ba.

Sanarwar ta ce “IGP a nasa jawabin ya kara da cewa tun kafin hawansa mukamin, magabata sun dauki matakin da ya dace wajen ganin an dawo da Patrick C. Okoli bakin aiki, wanda ya shigar da kara, kamar yadda kotu ta bayar.”

“Kamar yadda ya bayyana hakan, ta hanyar wata wasika a hukumance da ya aike wa hukumar ‘yan sanda kan amincewar babban sufeton ‘yan sanda na wancan lokacin, tun daga shekarar 2015, da kuma a gaban kotu na ranar 29 ga Nuwambar 2022, inda ya bukaci hukumar data fitar da wasikar maido da wanda ya shigar da kara sannan kuma ya aiwatar da karin girmarsa kamar yadda kotun ta bayar da kuma yin amfani da ikonsu na doka a kan haka.

“Saboda haka, bai kamata a ce dalilan da suka sa aka raina shari’ar ba, IGP ya kara tabbatar wa ‘yan Nijeriya irin jajircewarsa da tsayin daka wajen kare doka da kuma mutunta hukumomin shari’a don haka ba zai bijire wa duk wani umarni da ya dace da kotunan da suka dace ba.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *