“Mutanen da ke mutuwa sanadiyyar cuta mai karya garkuwar jiki sun ragu a ƙasarnan” – Boss Mustapha.

Sakataren gwamanatin tarayya Boss Mustapha ya ce mutanen da ke mutuwa sanadiyyar cuta mai karya garkuwar jiki sun ragu a ƙasarnan.

A lokacin taron tunawa da ranar yaƙi da cutar mai karya garkuwar jiki ta HIV/AIDS ta duniya, wanda ya gudana ranar Alhamis a Abuja, Mustapha yace mace-mace sun ragu daga kaso dubu 264,463 a 2015 zuwa dubu 51,000 a bana.

Boss Mustapha ya bayyana cewar an kuma samu raguwa a yawan mutanen da ke kamuwa da cutar.
Sakataren na gwamnatin tarayya ya buƙaci majalisun dokokin jihohi dasu amince da dokar haramta tsangwamar masu cuta mai karya garkuwar jiki.
domin ɗorewar nasarar da ake samu wurin yaƙi da cutar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *