“Gwamanonin jihohin kasarnan na sace kason kudaden da ake tura wa kananan hukumomi duk wata daga asusun tarayya” – Buhari.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamanonin jihohin kasarnan na sace kason kudaden da ake tura wa kananan hukumomi duk wata daga asusun tarayya.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamanonin jihohin kasarnan na sace kason kudaden da ake tura wa kananan hukumomi duk wata daga asusun tarayya.

Shugaban ya yi wannan zargi ne a taron manyan jami’an gwamnati na wannan shekara, na cibiyar nazarin manufofi da dabaru ta kasa (NIPSS) dake Kuru, a Jos.

A duk shekara dai masu yin kwas a cibiyar, sukan dauki wani muhimmin lamari da ya shafi kasa baki daya, su yi nazari game da shi, kuma a karshe su gabatar da sakamakon bincikensu da shawarwarinsu.

A bana sun duba batun mulkin kananan hukumomi ne bayan da Shugaban ya basu umurnin gudanar da nazari akan yadda ake gudanar da mulkin kananan hukumomi.

Mai magana da yawun shugaban kasar, Mallam Garba Shehu ya shaida cewar manyan jami’an gwamnatin sun kammala aikin nasu kuma sun bayar da shawarwari.

Shugaba Buhari ya ce a yanzu haka jihohi 20 ne kawai suke da zababbun shugabannin kananan hukumomi da jama’a suka zaba.

Yace wasu mulki akeyi a karkashin kantoma wanda ba zababbe bane kamar
yadda Garba Shehu ya bayyana.
Wasu daga cikin Gwamnonin kasarnan sun nesanta kansu daga zargin da
shugaban kasa yake yi masu.
Gwamnonin jihohin Benue, Ebonyi, Kwara, Filato, Ogun da Ribas sunce
basa cikin wadanda shugaban yake magana

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *