Aisha Buhari: An Saki Aminu Muhammad Daga Gidan Yari.

A daren jiya Juma’a ne aka sako ɗalibin Jami’ar Tarayya ta Dutse, Aminu Adamu Muhammad daga kurkukun garin Suleja, wurin da wata babbar kotu ta aika da shi bisa tuhumar yin kalaman cin mutuncin matar shugaban Najeriya Aisha Buhari.

Aminu Adamu Muhammad


Kama wannan dalibin dai ya ja hankulan ‘yan Najeriya, har ta kai ga wasu na sukar matakin da hukumomi su ka ɗauka, inda a ɗaya ɓangaren kuma wasu ke kallon halin da ya shiga a matsayin izina ga matasan ƙasar masu yawan wallafa sakonni irin wannan a shafukan sada zumunta.

Matar Shugaban Najeriya Aisha Buhari ta janye ƙara da kuma tuhumar da take yi wa ɗalibi Aminu Muhammad, kamar yadda lauyansa ya shaidawa Manema labarai sai dai babu karin bayani game da dalilin da ya sanya Aisha Buhari ta janye karar.


Matakin na zuwa ne bayan ɗalibin, wanda ke karatu a Jami’ar Tarayya da ke Dutse, ya shafe kwana uku a gidan yari da ke Suleja bisa umarnin kotu bayan ya ƙi amsa laifinsa.

Matar shugaban na zargin Aminu da ɓata mata suna saboda saƙon da ya wallafa a shafinsa na Twitter maƙale da hotonta tare da cewa “ta ci kuɗin talakawa ta yi bulbul”.

Ƙungiyoyin kare haƙƙi da masu sharhi sun soki Aisha game da matakin da ta ɗauka bayan rahotanni sun yi zargin cewa sai da aka lakaɗa wa Aminu duka kafin gurfanar da shi a gaban kotun.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *