Sha’aban Sharada yayi magana kan hana ‘Yan adaidaita sahu bin manyan titunan a Kano.

Dan takarar gwamna a jam’iyyar adawa ta ADP a jihar Kano kuma dan majalisar wakilai a mazabar karamar hukumar mulki ta tarayya Honorabul Sha’aban Ibrahim Sharada OON, ya soki matakin haramtawa masu sana’ar tuka babur mai kafa uku a jihar nan hawa wasu manyan tituna na gwamnatin jihar Kano.

Honarabul Sha’aban Ibrahim Sharada ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da kakakin majalisar yakin neman zaben gwamnan Abbas Yushau Yusuf ya raba wa manema labarai a Kano.

An ruwaito cewa Honarabul Sha’aban Ibrahim Sharada ya ce a daidai lokacin da ya kamata gwamnati ta fito da wani tunani na shawo kan matsalar matasa da kuma karkatar da hankalinsu daga aikata miyagun laifuka da shaye-shayen miyagun kwayoyi a jihar da ta fi kowacce yawan jama’a a Najeriya, maimakon haka ta yanke shawarar zabar hanyar zalunci.

Honorabul Sharada, wanda shi ne shugaban kwamitin majalisar wakilai kan harkokin leken asiri da tsaron kasa, ya jajanta wa matafiya da masu tuka babur a kan irin wahalhalun da gwamnati ke ba su.

Ya ce duk da cewa tsarin sufuri a jihar Kano na bukatar gyara gaba daya, amma yadda gwamnati mai ci ke tafiyar da shi yana nuna rashin mutunta rayuwa da jin dadin al’ummar jihar Kano.

“Wannan matakin zai sa mata masu juna biyu, yara ‘yan makaranta, da ƴan ƙasa masu aiki tuƙuru yin tafiya a kafa, wanda zai haifar da asarar yawan aiki ko ma rayuka.”

“Bugu da kari, zai kawo koma baya ga tattalin arzikin masu adaidaita sahu, masu sana’ar abinci, masu gyarawa, masu sayar da man fetur da sauran kayayyakin gyara, da kuma miliyoyin al’ummar Kano da ke samun abin dogaro da kai daga aikin babur din.” Ya kara da cewa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *