Kotu ta tura wanda ya yi batanci ga Aisha Buhari, Aminu Muhammad, gidan yari.

Rahotanni sun bayyana cewa an gabatar da Aminu Muhammad da ake zargi da zaginuwargidan Shugaban Najeriya, Aisha Buhari gaban kotu jiya Talata, kuma tuni ma an garzaya da shi gidan yari.

Wani Lauyan dalibin mai suna C.K Agu ya tabbatar wa da manema labari cewa an gurfanar da wanda yake karewar a gaban wata kotu da ke Abuja babban birnin kasar, kuma bai amsa laifin da ake zargin shi da aikatawa ba.

Mr Agu ya ce tun ranar 25 ga watan Nuwamba suka nemi a bada Aminu beli amma hakan ba ta samu ba.

”Ko a zaman kotun na jiya mun sanar da alkali cewa mun bukaci yan sanda su ba da Aminu beli cikin lokaci amma ba su amsa mana cewa za su sake shi ba ko a akasin haka.”

”Akan haka muka bukaci kotun ta bada shi beli bisa dalilan rashin lafiya da kuma cewa zai fara jarabawa a makaranta ranar 5 ga watan Disamba. Kuma a yanzu kotun ta umurci rundunar yan sanda ta gabatar da bukatar belin da aka shigar da gaggawa don kotu ta samu damar sauraren bukatar yau ko gobe,” in ji CK Agu.

Tun da farko iyayen dalibi Aminu Muhammad sun fada wa BBC cewa za a gurfanar da dan nasu kotu yau Laraba, kafin daga baya lauyansa ya tabbatar da cewa an fara zaman jiya Talata, kuma za a sake wani zaman yau ko gobe don duba bukatar ba da shi beli.

Da aka tambayi lauyan inda Aminu yake a halin yanzu sai yace: ” yanzu haka yana tsare a gidan yarin Suleja kafin a saurari bukatar bada shi beli.”

Tsare Aminu Muhammad wanda dalibi ne a jami’ar tarayya da ke Dutse a jihar Jigawa ya tayar da kura musamman a shafukan sada zumunta, inda da dama ke zargin kama shi da tsare shi ba bisa ka’ida ba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *