“Shari’o’i sun yi wa kotun ƙolin ƙasarnan yawa, ciki kuwa har da waɗanda ba su taka kara sun karya ba” – Mai Sharia Olukayode Ariwoola

Alƙalin alƙalan kasarnan,mai shari’a Olukayode Ariwoola ya ce shari’o’i sun yi wa kotun ƙolin ƙasarnan yawa, ciki kuwa har da waɗanda ba su taka kara sun karya ba.

Babban mai shari’ar ya bayyana haka ne a Abuja, lokacin wani taro nanmusamman na ƙaddamar da shekarar shari’a ta 2022 zuwa 2023, da kuma rantsar da manyan lauyoyi 63 na ƙasar.

A cewar alƙalin wasu daga cikin shari’o’in ba su cancanci a kaisu kotun ta ƙoli ba.

Yana mai cewar akwai buƙatar a tunatar da ƴan Najeriya cewar ya kamata su daina yawan shigar da ƙararraki, a maimakon haka, su rinƙa bin wasu hanyoyin sulhuntawa domin rage wa kotuna nauyi.

Ya ƙara da cewar “ƴan Najeriya, musamman ma ƴan siyasa ne waɗanda suka fi shigar da ƙara a faɗin duniya.

A lokacin da yake bayani kan alƙaluman, mai shari’a Ariwoola yace akwai ƙararraki 6,884 da aka ɗaukaka zuwa kotun ƙoli waɗanda ba ayi aiki a kansu.
ba har yanzu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *