Ministan Noma da Raya Karkara, Mohammed Mahmud Abubakar ya ce babu wata barazanar yunwa a Najeriya saboda mutane na da isasshen abinci a rumbunansu.
Ya ba da tabbacin ne a Abuja yayinda jawabi kan nasarorin gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari karo na biyar.
Da yake amsa tambayoyin manema labarai akan hauhawar farashin kayayyaki, Ministan ya ce, “Hakika akwai wadataccen abinci a kasar nan, duk da yadda aka samu karin farashinsu a kasuwanni.
A cewar ministan kasarnan na noma isasshiyar shinkafa, kasancewar sune na daya a nahiyar Afirka wajen nomanta, haka ma abin yake a fannin rogo da doya.
A bangaren noman dawa kuwa, kasarnan ce ta biyu a duniya bayan Amurka, kuma na uku a noman gero a duniya.
Sai dai Ministan ya alakanta tsadar takin zamanin da ake fama dashi a bana kan annobar COVID-19 da sauyin yanayi da kuma rikicin Rasha da Ukraine.
Mohammed ya kuma ce a ranar 12 ga watan Disamba mai zuwa ne gwamnatin tarayya za ta gudanar da wani taron shiyya-shiyya kan rikicin manoma da makiyaya.
Ya kuma ce gwamnatin za ta ci gaba da aikin gina rugage da burtalolin kiwo na zamani ga makiyaya.
A cewarsa, tuni aka riga aka ware wurare 16 a jihohi takwas a matsayin cibiyoyin kiwon dabbobi na kasa, kamar yadda yake kunshe a Daftarin Kiwon Dabbobi na Kasar